Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Dakarun Juyin Musulunci na Iran sun fitar da wata sabuwar sanarwa, a cikinta ta ce: "Ya ku Al’ummar Iran Musulunci masu girma da jarumtaka; Tsayin dakarku na musamman yana sa gaskiya kowace rana ta ƙara haskakawa a duniya, kuma yana ƙara ware zalunci da girman kai. Haka kuma yana sa mayaƙa su ƙara fata ga nasara ta ƙarshe, kuma yana saka yanke kauna a zukatan makiya bil'adama.
'Ya'yanku masu kishi a na rundunar sararin samaniya ta dakarun juyin musulunci, a ci gaba da ayyukansu na ladabtarwa, a zagaye na ashirin da bakwai na aikin Nasr 2, da kiran suna mai albarka na "Ya Aba Salihil-Mahdi, ka taimake ni," sun sake kai wani hari mai halakarwa a kan sansanin Amurka a Al-Azraq a Jordan, kuma sun haifar da barna mai yawa ga jiragen yaƙi da dama, haka kuma sun lalata wurin zama na sojojin Amurka, wanda ya haifar da mutuwa da raunin wasu daga cikinsu.
Amurka mai kashe yara yana ƙarya a fili ga al'ummarsa da sauran mutane game da adadin wadanda suka mutu, kuma muna kira ga cibiyoyin bincike da kafofin yada labarai da su gudanar da bincike a fagen game da wannan.
A wani hari na bazata, mujahidan Musulunci sun lalata na’urar tsaron sama nau'in Patriot da balloon leken asiri na Amurka mai kashe yara a Arbil, kuma sun kai hari a kan wurin zama na 'yan ta'addan Amurka.
Idan haramtacciyar gwamnatin Amurka mai girman kai ta ci gaba da ayyukanta na ta'addanci, za ta fuskanci martani mabanbanta".
…………….
Ra'ayinka